Connect with us

Labarai

Majalisar Nasarawa Ta Bukaci Gwamnati Ta Kai Dauki Ga Wadanda Iftila’in Guguwa Ya Shafa

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci Gwamnatin Jiha da kananan hukumomin jihar goma sha uku da su gaggauta bayar da kayayyakin tallafi ga wadanda guguwar iska ta shafa a fadin jihar.

Majalisar ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin inganta rayuwar wadanda abin ya shafa da rage musu radadin halin da suke ciki.

Shugaban Majalisar, Dr. Danladi Jatau, ne ya bayyana hakan bayan Hon. Hudu A Hudu ya gabatar da batun a matsayin lamari mai muhimmanci ga jama’a, yayin zaman majalisar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.

Shugaban majalisar ya ce abin jimami ne kwarai yadda guguwar iska ta lalata gidaje, makarantu, gine-gine da wasu muhimman kayayyaki da suka kai daruruwan miliyoyin Naira tare da jikkata mutane da dama.

Ina godiya da wannan kuduri da Hon. Hudu A Hudu ya gabatar domin wannan iftila’in ya shafi mazabata kai tsaye, inda guguwar ruwan ta rushe dakin jarrabawa na GSS Bassa. Har ila yau, kusan dukkan mazabu a fadin jihar sun fuskanci wannan matsala kamar yadda yawancin ‘yan majalisa suka bayyana.

Shawarar mu ita ce, dukkan shugabannin kananan hukumomi 13 na jihar su tattara bayanan gine-gine da mutanen da abin ya shafa tare da nemo hanyoyin da za a tallafa musu.

Muna kira ga Mai Girma Gwamna da ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar NASEMA da ta gaggauta daukar mataki ta hanyar raba kayayyakin tallafi ga wadanda abin ya shafa,” in ji shi.

Har ila yau, majalisar ta bayyana cewa guguwar ta bar iyalai da dama cikin kunci yayin da wasu ke kwance a asibitoci.

Tunda farko, Honarabul Hudu A Hudu, dan majalisa mai wakiltar Mazabar Awe Arewa, yayin da yake gabatar da batun, ya ce al’ummar Mahanga da ke mazabarsa da wasu yankuna sun rasa matsugunansu sakamakon guguwar.

Wannan lamari ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum matuka, inda gidaje fiye da 30 da mutane 500 suka samu matsala.

“Ina kira gare ku da ku goyi bayan wannan kuduri domin gwamnati ta zo ta taimaka wa mutanena.” Inji shi

 

Daga Aliyu Muraki

 

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara