Labarai
NUJ Jigawa Ta Nada Wakilin Rediyon Tarayya A Matsayin Mamba Na Musamman
Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa ta naɗa Kwamared Sani Muhammad Gumel da Kwamared Usman Mohammed Usman a matsayin mambobin majalisar kungiyar na musamman (Ex-Officio).
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar ta kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed, ta sanya wa hannu kuma ta rabawa manema labarai a Dutse.
Ta bayyana cewa, an yi waɗannan naɗe-naɗen ne a matsayin girmamawa da yabo ga jajircewarsu, ƙwarewa, da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen haɓaka aikin jarida a Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya.
Aisha Abba Ahmed ta ƙara da cewa, duka waɗannan mutane biyu sun dade suna nuna ƙwazo da biyayya ga manufofi da burin ƙungiyar.
Ta ce, ana sa ran waɗannan mambobin na musamman za su yi aiki kafada da kafada da majalisar, domin tallafa wa shirye-shiryenta, da bayar da shawarwari, da kuma ƙarfafa hulɗa da burin ƙungiyar a fadin jihar.
Ta ce, kungiyar ta buƙaci dukkan mambobi da su ba su haɗin kai da goyon baya wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Sakatariyar ta ƙara da cewa, naɗin ya fara aiki nan take.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
