Labarai
Majalisar Kaduna ta Amince da Kudirin Kula da Lafiyar Kwakwalwa na Jihar
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin kafa sashen kula da masu fama da matsalar kwakwalwa a jihar ya zama doka.
Dokar za ta samar da kariya da kuma bunkasa ‘yancin masu fama da matsalar kwakwalwa musamman masu tu’ammuli da muggan kwayoyi a fadin jihar Kaduna.
Da yake jagorantar zaman majalisar, shugaban majalisar dokokin jihar kaduna, Yusuf Dahiru Liman ya sanar da amincewa da kudirin wanda aka yiwa lakabi da kudirin kula da lafiya masu fama da cutar kwakwalwa na jihar Kaduna.
Da yake gabatar da rahoto, shugaban kwamitin hadin gwiwa na lafiya da sharia, wanda aka dorawa alhakin yin nazari a kan wannan kudiri, Mr. Haruna Barnabas ya ce sun yi nazarin kudirin sannan sun gano cewa akwai bukatar a karfafa matakan da jihar ke bi wajen kula da masu fama da matsalar kwakwalwa domin bunkasa lafiyar kwakwalwa da magance kalubalen da masu tu’ammuli ke fuskanta a cikin al’umma.
Ya ce sabuwar dokar za ta taimaka wajen sauya suna tare da manufofin Hukumar Yaki da Tu’ammuli da Muggan Kwayoyi ta Jihar Kaduna-KADBUSA zuwa Hukumar Yaki da Tu’ammuli da Muggan Kwayoyi da Kula da Lafiyar Kwakwalwa ta Jihar Kaduna-KADSAMHSA domin ya dace da yadda ake tafiyar da irin wadannan ayyuka a matakin duniya.
A cewar shugaban kwamitin, za ta tabbatar da cewa ana mutunta masu tu’ammuli da muggan kwayoyi, da gyara dabi’un su da kuma sake shigar da su cikin al’amuran al’umma don su bada gudunmuwa mai ma’ana.
A wani labarin kuma, majalisar dokokin jihar Kaduna ta mika wani kudiri dake bukatar kafa Hukumar Kula da Ilimin Manyan Makarantun Sakandare, na 2025.
Kudirin, wanda dan majalisa mai wakiltar birnin Zaria a majalisar dokokin jihar Kaduna, Barrister Mahmud Lawal Isma’ila ya ce kudirin zai inganta tsarin ilimin jihar ya dace da ci gaban zamani.
Ya ce idan aka amince da kudirin ya zama doka, hukumar za ta rika kula da dukkanin manyan makarantun sakandare a fadin jihar, don tabbatar da ganin ana sarrafa kudaden da aka ware ma bangaren ilimi don ganin ya habbaka.
Shamsuddeen Mannir Atiku
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
