Labarai
Gwamnan Zamfara Ya Amince Da Bada Albashin Wata Daya Kyauta Ga Ma’aikatanta
Gwamna Dauda Lawal ya amince da biyan albashin wata daya kyauta da aka fi sani da 13th months ga ma’aikatan jihar Zamfara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce shugaban ma’aikata na jihar ya sanar da amincewar ne a wata takardar da ya fitar a ranar 28 ga watan Disamban 2024.
Ta ce albashin shi ne irinsa na biyu a tarihin jihar Zamfara, inda gwamnatin Lawal Dauda ta biya na farko a watan Disambar bara.
Sanarwar ta ce, ma’aikatan gwamnati da wadanda suka yi ritaya za su samu alawus na kashi 30 bisa dari na albashinsu a matsayin albashinsu.
Sanarwar ta bayyana cewa, biyan alawus din na daya daga cikin dabaru da dama na karfafawa ma’aikata gwiwa da bunkasar tattalin arziki a jihar Zamfara.
Domin cika alkawuran da ta dauka, gwamnati ta biya sama da Naira biliyan 10 na giratuti da ake binta a cikin shekaru 11 da suka gabata, ta kuma amince da mafi karancin albashi na Naira 70,000, tare da tabbatar da biyan albashin ma’aikata kan lokaci.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
