Ilimi
Babu Gaskiya Ga Labarin Rashin Ingancin Makarantun Jihar Nasarawa – Peter
Gwamnatin Nasarawa ta karyata labarin da wata kafar yada labarai ta wallafa akan rashin ingancin kayan karatu a jihar.
Gwamnatin jihar nasarawa tace babu kamshin gaskiya a cikin rahoton da wara kafar yada labarai ta wallafa cewar yaran ‘yan-makarantan firamaren gwamnati suna karatu a kasa babu kujeru.
Rahoton bayanma babu labarin gaskiya da aka rubuta gwamnatin jihar na zargin an dauki nauyin kafar yada labarai ne domin yin adawa da ayyukan raya jihar da gwamnati maici ke gudanarwa a faɗin jihar, musamma ma a bangaren ilimi.
A wata sanarwa da mataimakin na musamman akan harkokin al’umma mista Peter Ahemba ya rabawa manema labarai a lafiya yace gaskiya ne wasu makarantu suna fama da karancin kayayyakin koyo dana koyarwa a wasu makarantu a jihar kamar yadda yake a kasashe masu tasowa, gwamnatin jihar nasarawa ta dauki kwararan matakai wajen samar da dukkannin ababen da ake bukata a sashin koyo dana koyarwa, gyaran makarantu, Gina wasu sabbi harma da samar kujerun zama ga dalibai da dai-dai sauransu.
Sanarwan tayi bayanin cewar ko a kwanakin Gwamnan jihar nasarawa Abdullahi Sule ta hannun hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar ya raba daruruwan kujerun zama dana rubutu dama takardun rubutu da karatu a faɗin jihar.
Sanarwan ta kara da cewar, gwamnatin jihar zata cigaba da katange makarantu ta na firamare da sakandare hadi giggina fanfunan burtsatse dama Sauran ababen more rayuwa domin ‘ya’yansu Daman karatu cikin inganci da natsuwa.
Hakazalika, ta bukaci al’umma da suyi watsi da wannan rahoton da cewar baida tushe balle makama, inda ta hori ‘yan-jaridu da a koda yaushe kafin su wallafa labarinsu su tabbatar sunyi cikakken bincike a hannun jami’an gwamnati domin gudun yada labarai kanzon kurege.
Kana sanarwan ta bada tabbacin gwamnatin jihar nasarawa wajen samar da dukkannin ababen da ake bukata don inganta ilimi hadi da bunkasa walwalan malamai basu horo, daukan wasu sabbi malamai aiki dama cigaba da biyan albashi akan lokaci.
Rel/Aliyu Muraki/lafiya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
