Labarai
Sanata Yari Ya Himmatu Wajen Sake Tsugunar Da Iyalai 4000 Da Suka Rasa Muhallansu
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar, ya kaddamar da aikin sake gina gidaje sama da 4,000 da ambaliyar ruwa ta lalata a karamar hukumar Gumi ta jihar Zamfara.

A lokacin da yake kaddamar da aikin a garin Gumi, Sanata Yari ya ce kayayyakin aikin sun hada da manyan motoci guda 200 na Siminti, da bandir na rufin kwano 7,500 da wasu kudade ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta shafa a daminar bana.
Sanatan wanda ya samu wakilcin kwamishinan hukumar kidaya ta kasa jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Muttaka Rini, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin aiwatar da ayyukan, ya ce tun farko kwamitinsa ya tantance irin barnar da ambaliyar ruwan ta haddasa, a kokarin da ake na sake gina gidajen.

Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, ya ce an kasa wadanda abin ya shafa gida uku, bisa la’akari da girma da yawan dakunan da ke cikin gidajensu.
A cewarsa, kwamitin ya raba wadanda abin ya shafa gida uku inda rukunin farko ke da gidaje 706 da ke da dakuna 11 zuwa 15, sai rukuni na biyu mai dakuna 7 zuwa 9, yayin da rukuni na uku suka rasa dakuna 1 zuwa 6 a sakamakon iftila’in.

Ya bayyana cewa, a kashin farko na aikin an baiwa wadanda abin ya shafa wasu kudade da siminti, don fara aikin sake gina gidajensu, yayin da kashi na biyu kuma za su sami katakai da kwanan rufi.
Sanata Abdul’azeez Yari ya ci gaba da cewa, ya kuma kafa wani karamin kwamiti da zai sa ido domin tabbatar da bin ka’ida da aiwatar da kashi na farko na aikin, da suka hada da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a matsayin mambobi.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Gummi, Mai Shari’a Lawal Hassan mai ritaya, ya yabawa Sanata Abdulaziz Yari Abubakar bisa jajircewarsa wajen gudanar da ayyukan sake gina al’umma.
Sarkin ya ba da tabbacin cewa majalisarsa ta kuduri aniyar yin aiki tare da kwamitin aiwatar da ayyukan, da nufin tabbatar da sake gina matsugunan da aka rasa.

Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

