Labarai
Allah Ya Yi Wa Dan Gwamnan Jigawa Rasuwa
Allah Ya yi wa Abdulwahab Umar Namadi, dan gwamnan jihar Jigawa rasuwa.
Marigayin ya rasu ne da yammacin yau Alhamis sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Dutse zuwa Kafin Hausa a jihar ta Jigawa.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse ya bayyana cewa, Marigayi Abdulwahab mai shekaru 24 ya rasu ya bar iyayensa da ’yan uwa da dama.
“Cikin alhini tare da mika wuya ga Allah, Mai Girma Gwamna Mallam Umar Namadi, na sanar da rasuwar babban dansa Abdulwahab Umar Namadi“.

Tuni aka yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, a garin Kafin Hausa.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Maryam Namadi ta rasu a jiya Laraba 25 ga watan Disamban 2024, a lokacin da yake ziyarar aiki a kasar China.

Da yammacin yau ne Gwamnan ya isa jihar Jigawa daga tafiyar.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
