Labarai
An Gargadi Jama’a Su Guji Zama A Muhallin Da Babu Isashshen Iska
Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Asibitin Jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya gargadi jama’a da su nisanci gidaje ko dakunan da ba su da isasun wuraren da iska zai shiga tare da kai rahoton duk wasu alamun da ba a saba gani ba a asibiti mafi kusa don daukar matakan da suka dace.
A cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Suleiman ta rabawa manema labarai ta ce, wani hadarin da mutane ke fuskanta ya hada da zazzabi mai tsanani, ciwon kai, amai da ciwon makogwaro, kasala da sauransu.
Ya ce ƙwararrun Ma’aikatan Lafiya (RRT) suna zaman ko ta kwana duk wuraren kiwon lafiya don magance duk wani al’amarin da ya taso na gaggawa.
“Saboda sauye-sauyen yanayi da cututtuka masu yawa, babban sakataren hukumar kula da asibitocin jihar Kano Dakta Mansur Mudi Nagoda yana shawartar jama’a da su yi taka tsantsan tare da ziyartar asibiti mafi kusa da zarar sun kamu da wata alama da ba a saba gani ba don guje wa bugun jini da ciwon sankarau.
“Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da, Zazzaɓi mai tsanani, ciwon kai, amai da ciwon makogwaro, gajiya da lallashi kamar sauran alamomin.
Abdullahi Jalaluddeen Kano/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
