Connect with us

Labarai

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Da Ake Zargi Da Kisan Abokinsa A Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu, bisa zargin kisan abokinsa Bello Bukar Adam wanda ma’aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki take wato KEDCO.

 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce a ranar 5 ga watan Mayu ne rundunar ‘yan sanda ta samu ƙorafin ɓatan Bello Bukar Adam mai shekara 45, wanda aka ce ya bar gida tun ranar 4 ga watan Mayun.

Sanarwar ta ce a ranar ne kuma ‘yan sanda suka samu rahoton tsintar gawar mutumin, wanda aka jefar a ƙauyen Bechi da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, inda nan take rundunar ‘yan sanda ta tura tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin DPO na ƙaramar hukumar, inda suka ɗauko gawar zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, likitoci kuma suka tabbatar da mutuwarsa.

Daga nan rundunar ‘yan sanda ta ƙaddamar da bincike tare da kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu mai shekara 35 da ke unguwar Hotoron Arewa bisa zargin aikata laifin.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce a lokacin da ‘yan sandan ke tuhumar wanda ake zargin, ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutum biyu wajen fito da Bello,  wanda ya kasance abokinsa ne  daga gidansa.

Sadiq ya shaida wa ‘yan sanda cewa da kansa ya ɗaure Bello inda suka rika dukansa da sanduna da ƙarafa masu kaifi a kansa da sauran sassan jikinsa har sai da ya mutu.

Bayan ya mutu ne suka sanya shi jikin but ɗin motarsa, tare da jefar da gawar a kan titin Eastern Bypass, a daidai ƙauyen Bechi, inda suka gudu da motar, ƙirar Toyota Corolla 2015, da kuma wayar marigayin’‘, kamar yadda sanarwar ‘yan sandan ta yi bayani

Haka kuma wanda ake zargin ya shaida wa ‘yan sandan cewa dalilinsu na aikata hakan shi ne marigayin ya karɓi kuɗi har naira miliyan uku daga wajensa da nufin zai sama masa aiki, amma sai daga baya ya fahimci cewa marigayin ba zai sama masa aikin ba, kan hakan ne ya haɗa baki da wasu mutum biyu domin kashe shi tare da yin awon gaba da motarsa, inda suka ɓoyeta a wani gareji da ke unguwar Hotoro.

Tuni dai ‘yan sanda suka kwato motar.

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara