Connect with us

Kasuwanci

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Published

on

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma wajen dakile yaduwar kwarin nan da ke lalata tumatur a gonaki.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a wata hira da gidan rediyon Najeriya a Kano.

A cewar sa, kwarin sun mamaye gonakin tumatir a kananan hukumomin Bagwai da  Shanono da  Kura da  Garin Malam da Bebeji, Bunkure da Rano da  Kibiya da kuma wasu sassan Tudun Wada Dawakin Kudu.

Maibreadi ya bayyana cewa, rahoton da AFAN ta samu daga sassan kananan hukumomin ya nuna cewa gonakin Tumatir da suka kai hekta dubu hudu da dari shidda da ashirin da daya da kudinsu ya kai Naira biliyan daya ne a halin yanzu suka kamu da cutar, yana mai jaddada cewa idan ba a yi wani abu don ceto lamarin ba, nan da mako daya zuwa biyu masu zuwa, manoma za su yi asarar kusan Naira miliyan dubu goma  zuwa dubu ashirin a Kano.

Abin takaici shine akasarin manoman sun gama kashe kudi a gonakinsu, kuma shuka ta yi kyau, an kusa girbi sai kuma ga cutar ta bulla.”

Maibreadi ya jaddada bukatar gwamnati ta taimaka wa manoma da ingantaccen iri mai jure wa yanayi, yana mai cewa, manoman Kubewa suma sun sami bullar irin wannan annoba a kakar noman da ta gabata.

Mu manoma ba mu da ikon samun wadannan irin shuka, amma idan gwamnati ta hada hannu da kamfanonin kasa da kasa, za su iya saye su sayar da su, ko kuma ba da tallafi ga manoma domin gujewa irin wannan babbar asara da ke kara shafar tattalin arzikin kasar.”

Shugaban ya bukaci manoma da su daina amfani da maganin kwari mara inganci domin gujewa asara.

Khadija Aliyu

Labarai

Labarai3 days ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Labarai3 days ago

‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin...

Labarai3 days ago

Tinubu Zai Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki

  Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin...

Ilimi3 days ago

Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya

  Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya...

Labarai4 days ago

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423...

Labarai4 days ago

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai...

Labarai5 days ago

Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya...

Labarai5 days ago

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya

Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin...

Labarai5 days ago

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron...

Labarai5 days ago

Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar ‘yan jaridu a aikin Hajjin 2024....

Mafi Shahara