Labarai
Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano Ta Sake Gurfanar Da Ganduje Gaban Kuliya
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauraron korafe-korafen jama’a ta jihar Kano ta shigar da sabbin tuhume-tuhume kan almundahana a kan tsohon gwamnan jihar Dr. Abdullahi Ganduje.
Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana hakan a shirin da yayi a wani gidan talabijin mai zaman kasa a ranar Talata, inda ya zargi gwamnatin Ganduje da karkatar da kudaden al’umma.
Ya bayyana cewa, bincike ya nuna yadda aka karkatar da naira biliyan hamsin da dayada miliyan dari uku na kudaden kananan hukumomi zuwa wasu asusun ajiya da basu da hurumin karbar irin wadannan kudaden.
A cewar Muhuyi, gwamnatin Ganduje na cire naira biliyan 1 a duk wata daga asusun jihar ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma yi ikirarin cewa, an zuba Naira biliyan 4 ga asusun wani kamfanin noma daga asusun tattara harajin jihar ba tare da wani dalili ba.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
