Labarai
’Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 100 Kudin Fansa Kan Kowane Mutum Ɗaya da Suka Sace a Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u
‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka sace a cocin.
Shugaban al’umma kuma Olori Eta na Eruku, Cif Olusegun Olukotun, wanda mutane huɗu daga cikin danginsa suka kasance cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida.
Olukotun ya ce yana cikin coci tare da mutane biyar na danginsa lokacin da lamarin ya faru, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin yaran da yake kula da su ya tsere ta tagar cocin.
Ya tabbatar da cewa masu garkawan sun kira waya suna neman naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa na kowanne daga cikin mutane 38 da suka sace.
Olukotun ya yi kira da a ƙara tsaro a Eruku, wanda ke kan iyaka, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
