Labarai
Shugaban Kenya Ya Yi Watsi Da Dokar Da Ta Haifar Da Zanga-zanga A Kasar
Shugaba William Ruto na Kenya ya yi watsi da dokar fadada haraji da majalisar dokoki ta amince da ita, abin da ya haifar da zanga-zanga a kasar, inda ya sake mayar da dokar majalisar domin gyare-gyare.
Majalisdar tana zama na musamman karkashin tsauraran matakan tsaro, inda majalisar ta amince da tura sojoji domin kare gine-gine masu muhimmanci lokacin zanga-zangar.
Tun farko Kungiyar likitoci ta kasar ta tabbatar da mutuwar fiye da mutane 20 kana wasu kimanin 30 suka jikata sakamakon zanga-zangar da aka fuskanta a fadin kasar a wannan Talata da ta gabata, domin kiyayya bisa sabuwar dokar da majalisar dokokin kasar ta amince ta fadada haraji kan kayayyaki a kasar.
Wannan na zuwa lokacin da masu zanga-zangar ke cewa za su sake komawa kan tituna a gobe Alhamis, domin nuna girmamawa ga masu zanga-zangar da suka mutu lokacin artabu da jami’an tsaro, kamar yadda masu shirya zanga-zangar suka nuna a shafukan sada zumunta musamman na X ko kuma Twitter.
Ana sa bangaren Shugaba Ruto na kasar ta Kenya ya yi zargin cewa masu tayar da zaune tsaye sun karbe ragamar zanga-zangar.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
