Fasaha
Shirin Fitar ‘Yan Nijeriya Miliyan 50 Daga Talauci Zai Tabbata – Idea Lab
Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar kungiyar Idea Lab sun tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shirin da gwamnatin yanzu ta yi na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan hamsin daga kangin fatara zai kasance gaskiya.
Kungiyar Idea Lab Agency tare da hadin gwiwar Bankin Masana’antu, Babban Bankin Najeriya da sauran Hukumomin Gwamnati sun kuduri aniyar ganin an cimma wannan kyakkyawar manufa ta Shugaba Bola Ahmad Tinubu kafin 2027.
Babban jami’in kungiyar Idea Lab Organisation Mr Rex Emmanual ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske kan ayyukan kungiyar kan shirye-shiryen raya kasa.
Mista Rex ya ce Idea.Lab tare da hadin gwiwar Bankin Masana’antu, Babban Bankin Najeriya da Bankin Duniya suna zaburar da ‘yan kasa don sanin yadda ake samun tallafi da lamuni a fadin duniya don bunkasa tattalin arziki ta hanyar kanana da matsakaitan masana’antu.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana haɗin gwiwa tare da wasu cibiyoyi na kuɗi a matsayin ingantattun dandamali don bada duk tallafi kuma a shirye suke su ga ‘yan Najeriya masu sha’awar Tattalin Arziki na Kasuwancin zamani ya tabbata.
Mista Rex ya ci gaba da bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kirkiro wannan tsarin ne domin amfanin kananan kamfanoni da matsakaitan masana’antu don samun irin wannan lamuni.
Babban kodinetan na kasa ya yi imanin cewa hakan zai taimaka wajen fitar da ‘yan Najeriya miliyan hamsin daga kangin talauci bisa manufar gwamnatin tarayya.
A cewar kodinetan na kasa, shirin na Lab yana da goyon bayan Bankin Masana’antu da Gwamnatin Tarayyar Najeriya don horar wa, shiryawa da daukar wakilai da masu cin gajiyar ayyukan yi a cikin gida da waje.
Ya ce babban bankin kasar da sauran bankunan kasuwanci sun shigo ne saboda shirin ya kunshi kudi, don haka mutane za su iya samun lamuni ta hanyar wakilai da taimakon tallafin karatu da sauran ayyukan fasaha.
Bashir Mayere/Wababe
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
