Labarai
Sarkin Birnin Gwari Ya Yaba da Tsarin Zaman Lafiya A Yankinsa, Yayi Kira Ga Manoma Su Ci Gaba Da Noma
Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Maigwari ya yaba da nasarar tsarin zaman lafiya da aka kaddamar a yankin kusan watanni goma da suka gabata, yana mai cewa ya dawo da kwanciyar hankali tare da karfafa wa manoma gwiwa su koma gonakinsu.
Da yake magana a lokacin ziyarar gani da ido domin duba yadda tsarin zaman lafiya yake a Birnin Gwari, Sarkin ya ce yarjejeniyar zaman lafiya—wadda ta samu da haɗin gwiwar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Gwamnatin Jihar Kaduna, hukumomin tsaro da kuma wakilan ƙungiyoyin ’yan bindiga—ya taimaka sosai wajen rage matsalar rashin tsaro a yankin.
Ya bayyana cewa ko da yake har yanzu ana samun yan kwace kwace daga wasu miyagu amma lamarin tsaron yayi sauƙi sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.
Sarkin ya bayyana cewa a tarukan da aka gudanar da shugabannin al’umma, an shawarci manoma su koma gonakinsu duk da kalubale, ko da hakan na nufin amfani da taki na gargajiya a maimakon na zamani.
A cewarsa, da dama daga cikin manoma sun bi wannan shawara, abin da ya haifar da dawowar ayyukan noma a yankin saboda zaman lafiya da aka samu.
Alhaji Zubairu Maigwari ya jaddada cewa nan da shekara mai zuwa, ana sa ran karin manoma za su koma cikakke gonakinsu idan zaman lafiya ya ci gaba da inganta.
A tattaunawa da aka yi da Danmasanin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu AbdurRauf, ya bayyana cewa tsarin zaman lafiyar ya samar da damar zama tare, inda makiyaya da manoma ke aiki tare domin kare wannan yarjejeniya.
Ya kara da cewa harkokin tattalin arziki sun fara farfaɗowa a Birnin Gwari, inda al’ummomi da kansu ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ya kuma roki Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna su faɗaɗa tsarin zuwa wasu wurare masu fama da rikice-rikice, musamman ƙauyukan kan iyaka da ke fuskantar barazanar shiga daga jihohin makwabta.
Ya jaddada cewa irin tsarin tabbatar da zaman lafiya da akayi a Birnin Gwari zai taimaka wajen dakile matsalolin tsaro a yankunan kan iyaka tare da ƙarfafa ƙoƙarin zaman lafiya a fadin ƙasar nan.
A halin yanzu, an ziyararce yammacin Birnin Gwari—ciki har da Dam ɗin Fagoma da Sabon Layi da Gagumi da Kakangi da Kuma Randagi domin duba yadda manoma suka koma gonakinsu.
A matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar, tsoffin ’yan bindiga da al’ummomin yankin ana sa ran za su tashi tsaye domin kare yankinsu daga dukkan wani kallubalen tsaro.
PR: Adamu Yusuf
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
