Connect with us

Labarai

Hajjin 2025: Jami’an Kaduna Sun Sami Lambar Yabo Ta Kasa

Published

on

Jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna sun sami lambar yabo ta kasa bisa namijin ƙoƙarin da suka nuna a aikin Hajjin shekarar 2025.

Kafar yada labaran aikin Hajji ta Independent Hajj Reporters (IHR) ce ta bayar da lambar yabon a wani taro da aka gudanar a Abuja.

Jami’an Hukumar Alhazan ta Kaduna da aka  karrama sun haɗa da Hajiya Halima Lawal Babale, mai rikon mukamin Daraktan Sashen Gudanarwa da Kuɗi, da kuma Alhaji Surajo Umar, Shugaban Sashen Kula da Harkokin Kudi.

An yaba musu saboda sadaukar da kai da jajircewarsu wajen tabbatar da cewa Alhazan Kaduna sun samu kulawa, jagoranci da taimakon da ya kamata  tsawon lokacin da suke kasa mai tsarki.

Babban Sakataren IHR na kasa, Ibrahim Mohammed, ya yaba da gagarumar nasarar da suka samu, inda ya bayyana su a matsayin abin koyi ga sauran jami’ai, domin sun taimaka matuƙa wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi.

Haka kuma, an karrama wasu jami’an hajji daga jihohi daban-daban da kuma kamfanoni masu  zaman kansu da suka yi fice a aikin Hajji.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda Darakta-Janar na Gidan Rediyon Tarayya (FRCN), Muhammed Bulama ya wakilta, ya yaba wa IHR bisa ƙoƙarinta na inganta sha’anin gudanar da aikin Hajji.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin ci gaba da inganta walwalar alhazan Najeriya a ayyukan Hajji.

 

Safiyah Abdulkadir

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara