Ilimi
Gwamnatin Jigawa Za Ta Katange Makarantun Sakandare Domin Samar Da Ingantaccen Yanayin Karatu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bude tayin kwangila domin gina katanga, ƙofofi da gidajen masu gadi a wasu makarantun sakandare a fadin jihar.
A jawabinsa yayin gabatar da tayin, Shugaban Hukumar Manyan Makarantu na Jihar, Dakta Abubakar Sabo Yusha’u ya ce za a gina katanga da ƙofar shiga da gidan mai gadi a manyan makarantun sakandare ne domin kare makarantun daga mamayar filaye tare da samar da yanayin koyo da koyarwa mai kyau ga malamai da ɗalibai.
Dakta Abubakar Sabo Yushau ya bayyana cewa, ayyukan na daga cikin ajandar Gwamna Umar Namadi 12, wajen gyara sashen ilimi da inganta harkar koyo da koyarwa a makarantun jihar.

A cewarsa, manyan makarantun sakandare 15 ne za su ci gajiyar ayyukan, inda za a gina katanga, ƙofa da gidan mai gadi a kowace makaranta.
Ya kuma gode wa Gwamna Umar Namadi bisa jajircewarsa wajen inganta harkar ilimi a jihar.
Dakta Yushau ya bukaci waɗanda suka yi nasarar samun kwangilar da su ji tsoron Allah tare da tabbatar da ingantaccen aiki cikin wa’adin da aka kayyade.

A jawabansu, wakilan ƙungiyoyin kwararru na Due Process sun yi karin bayani kan ka’idoji da hanyoyin gudanar da tsarin kwangila, tare da kira ga ‘yan kwangila da su kiyaye dokokin tsarin kwangilar.
A jawabinsa na godiya a madadin hukumar, Daraktan Harkokin Gudanarwa da Kudi na, Malam Hussaini Ahmad Ubale ya gode wa hukumomi tare da yabawa kamfanonin da suka nuna sha’awa wajen shiga tsarin tayin kwangilar.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
