Labarai
Karamar Hukumar B/Gwari Ta Kare Kasafin Kudinta A Majalisar Dokokin Jihar Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna da karamar hukumar Birnin Gwari sun jaddada aniyarsu na karfafa hadin gwiwa domin kare rayuka da dukiyoyi a yankin.
Shugaban karamar hukumar Birnin Gwari Salisu Isah ya bayyana haka jim kadan bayan kare kudirin kasafin kudin shekarar 2026 da majalisar ta gabatar a gaban majalisar dokokin jihar Kaduna.
Alhaji Salisu Isah ya bayyana Birnin Gwari a matsayin wani yanki mai cike da tashin hankali da ke fuskantar kalubalen tsaro, inda ya jaddada bukatar gwamnati ta ci gaba da sanya ido a kai. Ya bayyana cewa majalisar ta gabatar da kasafin kudi sama da Naira biliyan 7 don inganta tsaro da samar da muhimman ababen more rayuwa a karamar hukumar da ta fi yawan masu noma.
A wani lamari makamancin haka, karamar hukumar Makarfi ta yi alkawarin ba da fifiko kan harkokin tsaro, ilimi, samar da lafiya da kuma ci gaban jama’a a kasafin kudi na shekarar 2026.
Shugaban karamar hukumar Garba Mohammed Sabon Gari ne ya bayyana haka a lokacin da yake kare kudirin kasafin kudin karamar hukumar a gaban kwamitin kasafin kudi da aiwatar da majalisar.
A cewarsa, majalisar ta ba da shawarar kashe sama da Naira biliyan 5 don inganta abubuwan more rayuwa da inganta zamantakewa da tattalin arziki a fadin yankin.
COV/SHAMSUDDEEN MANNIR ATIKU
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
