Connect with us

Labarai

NIPHID Ta Kaddamar da Gangamin Wayar da Kai Kan Cutar Kuturta a Kasuwannin Jihar Kaduna

Published

on

Daga Ibrahim Suleiman

Hukumar Kula da Lafiya da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NIPHID), da ke Saye a karamar hukumar  Zariya ta jihar Kaduna, ta gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a kasuwannin Giwa da Yakawada da  ke jihar, domin tunawa da Ranar Duniya ta Cutar Kuturta, tare da nufin wayar da kan jama’a game da rigakafi, gano cutar da wuri, da kuma maganinta.

A yayin gangamin, Daraktan-Janar na hukumar Abdullahi Dalhatu Aminu, ya ce an shirya aikin ne domin ilmantar da jama’a cewa cutar kuturta tana warkewa, musamman idan an gano ta da wuri.

Alamomin cutar sun hada da canjin launin fata—fari, ja, ko baki—sau da yawa ana kuma rasa jin zafi ko sanyi a wurin da cutar ta shafa,” in ji shi.

A don haka Dr. Aminu ya bukaci jama’a da su garzaya zuwa cibiyar lafiya mafi kusa idan sun lura da canje-canje a fata, yana mai jaddada cewa gano cutar da wuri na hana nakasa da kuma hana yaduwar cutar.

Ya kara da cewa Ranar Duniya ta Cutar Kuturta tana baiwa jama’a dama su dawo da martabar wadanda cutar ta shafa da kuma yakar wariya da rashin fahimta. “Mutanen da suka kammala magani sun warke gaba daya kuma ba za su iya yada cutar ba,” in ji shi.

An zabi karamar hukumar Giwa don yin wannan gangami ne saboda kididdigar da ake da ita na nuna cewa ita ce ke da yawan rahoton cutar kuturta a jihar, in ji Dr. Aminu.

A jawabinta, Dr. Umma Aliyu, Shugabar Sashen Asibitoci a NIPHID, ta shawarci marasa lafiya da ke kan magani da su bi ka’idojin shan magungunansu yadda ya kamata domin gujewa matsaloli ko dawowar cutar.

Shi ma a nasa jawabin, Sarkin Kasuwar Giwa, Malam Ibrahim Isa, ya bukaci jama’a da su kaucewa wariya da nuna bambanci, tare da karfafa goyon baya, fahimta da tausayi ga wadanda ke fama da cutar.

Wasu daga cikin marasa lafiya, ciki har da Yarima Dalladi Paul, Malam John, da Ayuba Kom, sun raba labaran kwarewarsu tare da rokon jama’a da su daina nuna wariya ga wadanda ke da cutar.

Taron gangamin ya hada da jawabai na lafiya da tattaunawa da al’umma domin inganta wayar da kai da kuma karfafa gwiwar mutane da su garzaya asibiti da wuri idan sun lura da alamominta.

Taken Ranar Duniya ta Cutar Kuturta na wannan shekara shi ne: “Cutar Kuturta  tana warkewa, babban kalubale shi ne nuna wariya.”

 

 

Labarai

Ilimi15 hours ago

Dr. Builder Muhammad Uba Ya Jagoranci Rangadin Makarantu a Birnin Kudu

Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dakta Builder Muhammad Uba ya bayyana ilimi a...

Labarai2 days ago

Masarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin

Daga Yusuf Zubairu Majalisar Masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna ta yi kira ga al’ummomin da ke Karamar Hukumar Lere...

Labarai2 days ago

Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kammala tanadin katin shaidar rigakafin cututtuka ga dukkan maniyyatan aikin Hajjin shekarar...

Labarai2 days ago

NEMA ta Karbi ‘Yan Najeriya 522 da Aka Dawo da su Daga Jamhuriyar Nijar

Daga Khadijah Aliyu Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi wani rukuni na ’yan Najeriya 522 da...

Labarai2 days ago

Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila – Iran

Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar...

Labarai2 days ago

Radio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya

An bayyana cikar shekaru 75 da kafuwar Radio Nigeria a matsayin wani babban mataki wajen gina ci gaban zamantakewa, tattalin...

Labarai2 days ago

Ɗaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano

Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Asibitin...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Sadaukar Da Albashinsa Domin Sabon Asusun Tallafi Ga Sojoji

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa wani asusun tallafi na musamman domin taimaka wa jami’an rundunar sojin...

Labarai2 days ago

FMC Gusau ta karɓi tallafin littattafan lafiya daga gidauniyar Sir Emeka Offor

Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya da ke Gusau, ya karɓi tarin littattafan kiwon lafiya da mujallu daga Sir Emeka...

Labarai2 days ago

NIPHID ta gudanar da gangamin wayar da kai kan tarin fuka a Zaria, Kaduna

Cibiyar kula da lafiya dake Saye Zaria, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar tarin fuka (TB) a...

Mafi Shahara