Labarai
Mutum 12 Sun Mutu A Rikicin Da Ya Biyo Bayan Zaben Shugaban Kasar Chadi
Hukumomin Chadi sun tura dakaru sassan kasar don su kwantar da tarzomar da ta barke bayan zaben shugaban kasar da aka yi, inda alkaluma ke nuna cewa adadin mutanen da suka mutu a ranar Asabar ya kai 12 a lokacin hada wannan rahoto.
Akalla mutum 90 aka samu tabbacin sun ji raunuka iri-iri a N’djamena, babban birnin kasar.
Gidan talbijin na Chadi ya ba da rahoton cewa an haramta ajiye makamai ko yin amfani da su a kasar wacce ke tsakiyar nahiyar Afirka.
Rahoton ya ce an haramta makaman ne bayan da aka samu asarar rayuka tara a daren Alhamis bayan da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 6 ga watan Mayu.
‘Yan sandan Chadi sun ce wasu mutane uku da suka ji rauni sun mutu a asibiti a N’djamena a daren Juma’a yayin da wasu fararen hula 30 suka ji rauni a wani fada da ya barke.
Shugaban mulki soja, Mahamat Deby ne ya lashe zaben shugaban kasar sai dai abokin hamayyarsa Succes Masra na kalubalantar sakamakon.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
