Labarai
Mutane Sama Da Miliyan 5 Ne Za Su Amfana Da Tallafin Abinci A Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta kudiri aniyar bada tallafin kayan abinci ga mutane sama da miliyan biyar a karkashin shirin ciyarwa na watan Ramadan na bana.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rabon kayan abinci a karkashin shirin, gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya ce gwamnatin jihar tana sane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, don haka ta fito da tsare tsare daban-daban a karkashin shirin ciyarwa na watan Ramadan.

Ya bayyana cewa, manufar shirin ciyarwa a watan Ramadan ita ce domin a taimaka wa al’umma su samu abin da za su ci yayin da suka yi Azumi.

Tun da farko, kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Auwalu Danladi Sankara ya bayyana cewa, za a raba buhunan shinkafa masu dauyin kilogiram 25 guda dubu dari daya da hamsin, sai na masara shima buhu dubu dari da hamsin, da katan din taliya guda dari ga gidaje dubu dari da hamsin.

“Gwamnan Malam Umar Namadi ya amincewa ma’aikatar ta samar da cibiyoyin 590 a karkashin kwamitin shirin ciyarwa na watan Ramadan“.
A cewarsa, kowace mazaba gwamnatin jihar za ta kafa cibiyoyin bada tallafin guda biyu, tare da karin wasu cibiyoyi a masarautu biyar da wasu garuruwa.
Ya yi nuni da cewa, kowace cibiya za ta ciyar da mutane akalla 300 a kullum.
Ya ce, an kuma a samar da wani shiri na musamman na watan Ramadan ga ma’aikatan gwamnati, da jami’an tsaro, da masarautu da sauran cibiyoyin gwamnati a jihar, a matsayin wani mataki na karramawa daga gwamna Umar Namadi.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka zanta da gidan rediyon Najeriya sun yabawa Gwamna Namadi bisa wannan karamcin.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan

