Labarai
Masarautar Kauru Ta Bayyana Rashin Sha’awarta Kan Shiga Sabuwar Jihar Gurara
Wata kungiya mai zaman kanta Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, aka kuma raba wa manema labarai a Zariya.
A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma bata suna ne.
“Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu da zamantakewa a tsakaninmu da Masarautar Zazzau,” in ji shi.
Ya ci gaba da bayyana cewa Masarautar Kauru da Masarautar Zazzau na da alaka mai karfi ta fuskar kima da dabi’u da aka gada tun zamanin da.
Yayin da yake karin bayani kan dangantakar zamantakewa da ta tarihi, Malam Mukhtar ya bayyana cewa:
“Daga auratayya, zuwa hanyoyin kasuwanci, bukukuwa da tsarin shugabanci na gargajiya, dukkanmu muna da zumunci da mu’amala da jama’ar Zazzau. Kokarin cire mu daga wannan tsari da saka mu a wani sabon tsari ba zai haifar da alheri ba.”
Ya jaddada cewa Masarautar Kauru “ta yanke shawara a fili” cewa tana so ta ci gaba da kasancewa a cikin sabon tsarin Jihar Kaduna da ake shirin kafawa, tare da kin amincewa da duk wani yunkuri na saka ta cikin Jihar Gurara.
A karshe, Shugaban KECI ya bukaci masu rajin kafa Jihar Gurara, musamman daga Kudancin Kaduna, da su daina kokarin saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin jihar, yana mai bukatar a girmama ra’ayin jama’ar yankin.
Cov/Jibirin Zaria
-
Labarai4 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai2 days agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai6 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai5 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai5 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
