Labarai
Mahamat Idriss Deby Ya Lashe Zaɓen Chadi Da Gagarumin Rinjaye
Sakamakon zaben shugaban kasa a Chadi ya bayyana jagoran mulkin Sojin Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zagayen farko na zaɓen wanda ke nuna yiwuwar ya iya tsawaita wa’adin mulkin iyalan gidan Deby na wasu karin shekaru.
Zaben na ranar Litinin ya kawo karshen mulkin riƙon ƙwarya na shekaru 3 da Chadi ta fuskanta tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby Itno a fagen daga, wanda ya baiwa ɗansa Janar Mahamat Deby damar jan ragamar kasar mai fama da rikice-rikice baya ga ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta ANGE ta fitar ya nuna yadda Mahamat Deby da aka fi sani da Kaka ya lashe jumullar kashi 61.3 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa yayin da Firaministan ƙasar Success Masra ya samu kashi 18 da digo 53.
Kowani lokaci daga yanzu ne ake dakon kotun kundin tsarin mulki ta tabbatar da sahihancin zaɓen.
Sai dai tuni Firaminista Masra ya ƙalubalanci sakamakon, wanda ya bayyana da marar inganci.
A bangare guda tuni Shugaba Mahamat Deby Itno ya gabatar da jawabin kai tsaye ta gidan talabijin tare da godewa al’ummar ƙasar kan zaɓensa, tare da shan alwashin samar da yanayi mai inganci ga al’umma.
Tun gabanin sanar da sakamakon zaɓen an ga yadda dubunnan magoya bayan Deby suka fara murnar samun nasara a kan titunan birnin N’Djamena fadar gwamnatin Chadi.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
