Connect with us

Ilimi

Zaben Shugaban BUK: Farfesa Haruna Musa Ya Yi Wa Sauran ‘Yan Takara Zarra

Published

on

Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero Kano a harkokin karatu, kuma ƙwararre a fannin Kimiyyar Roba, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana a matsayin ɗan takarar da ya fi samun karɓuwa a zaɓen sabon Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK) da ake gudanarwa.

 

Sakamakon ya biyo bayan taron hadin gwiwar na bakwai (7th Congregation Parley) da aka gudanar a ranar Talata, 1 ga Yuli, 2025, inda Farfesa Musa ya samu ƙuri’u 853, ya bar sauran ‘yan takara hudu a baya da tazara mai yawa.

 

Tsarin zaɓen ya gudana  bisa nagarta da kulawa, wanda ya nuna goyon baya mai ƙarfi daga malamai da manyan ma’aikatan gudanarwa na BUK.

Farfesa Mahmoud Umar Sani tsohon Mataimakin shugaban jami’ar kan Harkokin Gudanarwa ya sami ƙuri’u 367, yayin da Farfesa Sani Muhammad Gumel (tsohon mataimakin  shugaban jami’ar kan harkokin karatu ya sami ƙuri’u 364, sai Farfesa Adamu Idris Tanko, tsohon mataimakin shugaban jami’a kan harkokin karatu da gudanarwa ya sami ƙuri’u 161, shi kuma Farfesa Bashir FaFaggya sami ƙuri’u 18.

 

Jimillar masu kada ƙuri’a da aka tantance su ita ce 1,784, inda shugaban kwamitin zaɓe, Farfesa Muhtari Ali Hajara, ya bayyana cewa ƙuri’u 17 ba su da inganci yayin da guda huɗu ba a bayyana su ba.

 

Da yake jagorantar taron, Shugaban jami’ar mai barin gado, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya jaddada cewa ko da yake ƙuri’ar amincewar jama’a tana da kaso 20 bisa dari, cikin tsarin zaɓen gaba ɗaya, tana taka muhimmiyar rawa wajen shawarwarin da kwamitin gudanarwar jami’ar zai yanke.

 

Wannan tsari yana nuna ƙarfin tsarin dimokuradiyya da gaskiya da jami’ar mu ta tanada.” In ji shi

A wani mataki na nuna ɗabi’ar kishin jami’a, ɗaya daga cikin fitattun ‘yan takarar, Farfesa Sani Muhammad Gumel, ya amince da sakamakon zaɓen, inda ya bayyana shi da cewa “an gudanar da shi bisa gaskiya da adalci ” tare da alkawarin ba da cikakken goyon baya ga Farfesa Haruna Musa.

 

Tsohuwar Ministar Ilimi, Farfesa Rukayyatu Ahmed Rufa’i, da tsohon Shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Abdalla Uba Adamu, sun taya shugabannin BUK murna bisa kyakkyawan tsari da kuma cigaban jami’ar.

 

Yanzu dai, hukuncin ƙarshe na wanda zai zama sabon Shugaban Jami’ar BUK na hannun Kwamitin Gudanarwar Jami’ar, wanda zai yi la’akari da kwarewa, hangen nesa, ƙwarewar gudanarwa da kuma amincewar jama’a kafin yanke shawara.

 

Tsarin zaɓen ya samu yabo daga fitattun mutane a fannin ilimi.

 

Daga Khadijah Aliyu

 

 

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara