Labarai
An Dakatar Da Shugaban APC A Jihar Nasarawa Bisa Zargin Cin Amanar Jam’iyya
Jami’an jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga Mazabar Gayam dake karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa sun dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Aliyu Bello, bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya.
Shugaban mazabar Gayam, Ibrahim Iliyasu ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
A cewar sa, daukar matakin dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar ya biyo bayan bincike kan koke-koken da mambobin mazabar suka shigar game da ayyukan cin amanar jam’iyya da shugaban ke aikatawa.
“Muna da kwararan shaidu da rahotannin da ke nuna cewa ya fito fili yana tallata dan wata jam’iyya daban, wanda hakan ya sabawa sashe na 21 (1), da na (2), da na(7) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar,” in ji shi.
“Muna sanar da dakatar da kai daga mukaminka nan take bisa karfin ikon da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bamu a karkashin sashe na 21 (D), (I), (111) bayan shawara da mu ka yi da masu ruwa da tsaki na mazabar,” in ji shi.
Ya bayyana cewa za su aika da sanarwar dakatarwar ga shugabancin karamar hukumar Lafia, kwamitin zartarwa na jihar da kuma kwamitin zartarwa na kasa domin tabbatar da dakatarwar tare da daukar mataki na gaba.
Alhaji Ibrahim Iliyasu ya kuma bukaci shugaban jam’iyyar da ya dakatar da bayyana kansa a matsayin mamba ko jami’in jam’iyyar har sai an kammala dukkan matakan da suka dace.
Dakatarwar ta zo ne jim kadan bayan kakakin jam’iyyar APC na jihar, Otaru Douglas, ya bayyana damuwa kan wani shiri da wani dan takarar gwamna a jam’iyyar ke yi na ganin an sauke shugaban jam’iyyar na jihar.
Daga Aliyu Muraki
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
