Labarai
Madatsar Tiga Za Ta Samar Da Ruwan Sha A Garin Rano
A kokarin magance matsalar karancin ruwan sha da garin Rano ke fuskanta na tsawon shekaru, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ta fara amfani da Madatsar Tiga don samar da ruwa mai a garin.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Dr. Muhammad Isa Umar, wanda ya kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Kano.
Gwamna Yusuf ya yaba wa Sarkin Rano bisa jajircewarsa wajen kare muradun al’ummarsa, inda ya tabbatar masa da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar ruwa a garin.
Ya bayyana cewa an riga an tsara shirin gina rijiyoyin burtsatse tare da hadin gwiwar ƙaramar hukumar, duk da cewa duwatsu da ke karkashin kasa na kawowa aikin cikas.
A kwanan nan ne gwamnatin jihar Kano ta gudanar da bincike domin tabbatar da lafiyar Madatsar ta Tiga, wacce za ta rika samar da ruwa a garin na Rano.
Haka kuma, madatsar tana dauke da tashar samar da wutar lantarki mai nauyin megawatt 10, wacce aka kammala gina ta a shekarar 2023.
Gwamna Yusuf ya nanata kudirin gwamnatinsa na ci gaba da inganta bangarori da dama, ciki har da noma, kiwon lafiya, muhalli, ilimi, da kuma karfafawa mata da matasa.
A nasa bangaren, Sarkin Rano, Ambasada Dr. Muhammad Isa Umar, ya gode wa Gwamna Yusuf bisa ci gaban da ake samu a masarautar, tare da rokon sa da ya ci gaba da mayar da hankali kan matsalar samar da ruwa.
Sarkin ya kuma yaba wa gwamnan bisa daukar mataki kan koke-koke da aka gabatar game da aikin titi mai nisan kilomita biyar, wanda hakan ya kai ga nusanya dan kwangilar da ya kasa yin aikin da wani wanda ya fi kwarewa.
Ziyarar gaisuwar Sallah ta kasance mai kayatarwa, inda aka gudanar da wasanni na gargajiya, ciki har da shahararrun mawakan garaya na Masarautar Rano, waɗanda suka nishadantar da jama’a.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
