Ilimi
Gwamnatin Jigawa Ta Yi Sabbin Nade-nade A Fannin Ilimi
Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar.
A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu.
“Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce mai kishin jasa da son cigaban ilimi da hidima ga al’umma,” in ji Sakataren Gwamnati.
Haka kuma, Gwamna Namadi ya amince da naɗa Hassan Nayaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Raya Ilimi ta Jihar Jigawa (JERA).
“Kafin wannan mukami, Nayaya ya kasance mukaddashin Shugaban Hukumar. Ya samu digiri a fannin Lissafi daga Jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 2000. Ya fara aiki a ma’aikatar ilimi ta Jihar Jigawa ne tun daga shekarar 1992, har ya kai matsayin Darakta a shekarar 2020,” in ji sanarwar.
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen suna daga cikin kokarin Gwamna na inganta shugabanci a fannin ilimi da ci gaban al’ummar Jihar Jigawa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an yi naɗin ne bisa cancanta, kwarewa da nagarta.
“Yayin da ake taya sabbin shugabannin murna, ana fatan za su yi aiki tukuru domin ba da gudunmawa ga ci gaban Jihar Jigawa.”
Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
