Labarai
Kwastam Ta Kama Kayayyakin Fasa Kwauri Na Naira Miliyan 478 A Kwara
Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Jihar Kwara, ta ce ta kama tare da kwace kayayyakin da aka haramta da kuma wasu da aka takaita shigowarsu cikin ƙasa da darajarsu ta haura naira miliyan 478 a bana.
Mukaddashin Kwanturola na Kwastam a jihar, Mataimakin Kwanturola Najeem Ogundeyi, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar a Ilorin.
Ya ce rundunar ta kuma samu kudaden shiga da suka haura naira biliyan 2.5 a cikin wannan lokaci da ake nazari, lamarin da ya ƙara tabbatar da rawar da take takawa wajen tallafa wa manufofin gwamnati na tattalin arziki.
A cewarsa, rundunar na da ƙudurin kare tattalin arzikin ƙasa tare da tabbatar da bin doka da oda.
Ogundeyi ya ce rundunar ba za ta bari jihar ta zama mafakar masu safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba, yana mai ƙara da cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin tauye tattalin arzikin ƙasa ta hanyar fasa kwauri zai fuskanci matakin doka.
Mukaddashin Kwanturolan ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba duk da gargaɗin da ake yi, musamman shigo da shinkafar waje, wadda ke barazana ga manoman cikin gida.
Ogundeyi ya ce haramcin shigo da irin wannan shinkafa daga ƙasashen waje wani mataki ne na ƙarfafa masu noma a gida, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa samarda abinci.
Ya ƙara da cewa nasarar waɗannan ayyuka ta samu ne sakamakon bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Mukaddashin Kwanturolan ya kuma yi kira ga mazauna yankunan kan iyaka, ’yan kasuwa da sauran jama’a da su haɗa kai da hukumar domin kare masana’antun cikin gida, bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.
Daga cikin kayayyakin da rundunar ta kama akwai motoci biyar da aka yi amfani da su, buhunan shinkafar waje guda 1,107, buhunan sukari da aka shigo da su 44, jarkoki 317 na man fetur (PMS), buhuna 120 na ma’adinin lithium da aka haƙo ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ɗaruruwan tufafin gwanjo da sassan gyaran motoci.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Labarai7 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Labarai7 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai4 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
-
Labarai4 days agoGwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya
-
Labarai4 days agoSojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina
-
Labarai7 days agoRamadan: Tinubu Ya Kara Jaddada Kudirinsa na Inganta Rayuwar Jami’an Soji
-
Labarai7 days agoTsarin Kundin Shirin Bunkasa Samarda Abinci Mai Gina Jiki
