Kasuwanci
Yan Sanda A Ilorin Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Aikata Laifuka
‘Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta kama wasu da ake zargi da aikata laifuka, ta kwato bindigogi, da kuma kama sama da Naira miliyan 11 da ake zargin kudin fansa ne a cikin wannan lokaci.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin.
A cewarsa jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar kungiyoyin tsaro na cikin gida sun cafke wani kasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Idirisu Sariki a Okuta, karamar hukumar Baruten.
Ojo ya ce ana kyautata zaton Sariki na da alaka da sace-sacen mutane da dama a yankunan kan iyaka a jihar
Ya bayyana cewa, a yayin samamen jami’an tsaro sun kwato bindiga kirar AK-47, harsashi 13, da wata mota kirar Volkswagen Golf da aka ce ’yan ta’addan na amfani da su.
Ya yi nuni da cewa a yankin Share, karamar hukumar Ifelodun, an kama wasu mutane biyu Suleiman Jamiu da Mumini Mohammed a hannunsu da kudi Naira miliyan 11.3, wadanda ake zargin sun samu ne daga satar kudin fansa.
Ojo ya ce an kama wasu gungun mutane uku da suka hada da Mohammed Olaiya Dende da Mohammed Dende bisa laifin yin garkuwa da mutane a ranar 30 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni a Oro.
Ya ce wadanda ake zargin za su fuskanci tuhuma da suka hada da hada baki, garkuwa da mutane, da kuma kisan gilla, bayan harin da aka kai a wata cibiya ta cashewa da wata unguwar da ta yi sanadin mutuwar mutum daya tare da sace wasu mutane shida.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
