Labarai
Kungiyoyin Alumma a Jigawa Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Gwamna Namadi Kan Lamarin Walida Abdulhadi
Daga Usman Muhammad Zaria
Wata ƙungiyar al’umma mai suna Hadejia Advocacy ta yaba wa Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, kan yadda ya shiga tsakani a lamarin Walida wadda ake zargin wani jami’in Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) mai suna Ifeanyi Festus Onyewuenyi da yin garkuwa da ita.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ceto yarinyar tare da jaririnta, waɗanda yanzu suke ƙarƙashin kulawar Gwamnatin Jihar Jigawa, wata babbar shaida ce da ke nuna ƙudirin Gwamna Namadi na kare rayuwa, mutunci da walwalar al’ummar jihar.

Shugaban ƙungiyar, Comrade Abubakar Babangida ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wani gangamin zanga-zangar goyon baya da aka gudanar a garin Hadejia.
Comrade Abubakar ya sake jaddada kudirin ƙungiyarsu na ci gaba da mara wa gwamnatin Gwamna Namadi baya domin ganin an bi wannan shari’a har zuwa ƙarshe, tare da tabbatar da an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci.

Sai dai masu zanga-zangar lumanar sun soki zanga-zangar da ƙungiyar ‘Hadejia Ina Mafita’ ta shirya, inda suka bayyana ta a matsayin wadda ke yaɗa bayanai marasa sahihanci da kuma ruɗar da jama’a, lamarin da ka iya haifar da rikici da hargitsi a cikin al’umma.
Sun kuma yi kira ga shugabannin Hadejia Ina Mafita da su riƙa yin taka-tsantsan yayin da suke magana ko sharhi kan irin waɗannan muhimman batutuwa, tare da gujewa siyasantar da su ko kuma ɓata sunan gwamnati.

Hakazalika, wata ƙungiyar mata mai suna Jigawa Women Development Initiative ta gudanar da zanga-zangar lumana a Dutse, babban birnin jihar, domin nuna farin cikinsu kan rawar da Gwamna Namadi ya taka a matsayin uba da jagora a lamarin Walida Abdullahi.
Ƙungiyar matan ta bayyana matuƙar damuwarta kan abin da ya faru, tare da nuna tausayi ga wadda abin ya shafa da iyayenta bisa irin mummunan cin zarafin da ake zargin wanda ake tuhuma ya yi mata.

Don haka sun yi kira ga al’umma gaba ɗaya da su haɗa kai wajen nuna goyon baya ga Gwamnatin Jihar Jigawa domin tabbatar da cewa an yi adalci ga Walida Abdullahi.
-
Labarai5 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai2 days agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai6 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai5 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
