Labarai
Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Wani Hatsari a Neja
Wani jirgin Sojin saman Najeriya ya yi haɗari jim kaɗan bayan tashi daga sansanin Sojin ƙasar da ke Kainji a jihar Neja, sakamakon tangarɗar inji.
Kakakin rundunar sojin saman na Najeriya Ehimen Ejodame lokacin da yake tabbatar da faruwar haɗarin ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar wannan haɗari, sai dai fasinjan da ke cikin jirgin yanzu haka suna karɓar kulawar gaggawa a asibiti.
Tuni dai aka jiyo hafson sojin saman Najeriyar Air Marshal Sunday Aneke, na yabawa matuƙan jirgin wanda ya bayyana da jajirtattu, da ya ce ƙwarewa da jarumtarsu ce ta tseretar da asarar rayuka a haɗarin.
Jiragen sojin Najeriya a lokuta da dama na gamuwa da haɗari wanda ke kaiwa ga asarar ɗimbin rayuka kama daga na sojojin da kuma fararen hula, dai dai lokacin da ƙasar ke buƙatar agajin sojojin na sama wajen yaƙi da matsalolin tsaron da suka dabaibaye ƙasar.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
