Connect with us

Labarai

Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jigawa Ta Bada Kiyasin Kasafin Kudi na Sama da Naira Biliyan 161

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026.

Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Babban Sakataren ya yi bayanin cewar, za a yi amfani da mafi yawan kudaden ne wajen gudanar da ayyukan hanyoyin mota tsakanin gariruwa da hanyoyin burji da kuma titunan cikin gari.

Yana mai cewar, haka kuma za a gudanar da ayyukan hanyoyi a manyan makarantun jihar ciki har Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa da kwalejin fasaha da ke Dutse da cibiyar binciken aikin gona ta Kazaure, da kwalejin koyon aikin lafiya matakin farko da ke Jahun da sauransu.

Sai dai kuma babban sakataren ya koka dangane da bukatar daukar injiniyoyi domin aiki a ma’aikatar da hukumar gyaran hanyoyin mota JIRMA da kuma daukar sabbin jami’an duba lafiyar ababen hawa wato V.I.O, idan aka yi la’akari da karancin ma’aikata saboda masu yin ritaya.

Alhaji Ahmad Isah ya kara da cewar ma’aikatar tana kokarin cimma yarjajjeniya da makarantar koyon tukin jirgin sama ta kasa da ke Zaria domin amfani da filin jirgin sama na Dutse a matsayin sansanin koyon tukin jirgin sama.

Kazalika, ya ce makarantar koyon tukun mota da ke karamar hukumar Birnin Kudu za ta amfana da wasu ayyuka a sabuwar shekara.

A nasa jawabin, shugaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Bulangu Alhaji Yusuf Ahmad Soja, ya yi addu’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya karfafa cigaban jihar nan a sabuwar shekara.

Labarai

Labarai3 days ago

Jigawa: Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kafa Kwamitin Tantance Bayanan Maniyyatan 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai tattara, tare...

Labarai4 days ago

Gwamnan Kano Ya Mika Sunayen Sabbin Kwamishinoni 2 Ga Majalisa Domin Tantancewa

Daga Khadijah Aliyu  Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zaɓi mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, da...

Labarai5 days ago

Durumbun Gusau Ya Bukaci Haɗin Gwiwa Wajen Magance Matsalar Tsaro

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Sabon Durumbun Gusau, Farfesa Aminu Ibrahim Gusau, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin...

Labarai5 days ago

Gwamnatin Neja Ta Jaddada Ƙudurinta Na Farfaɗo Da Kamfanin Buga Takardun Gwamnati

Daga Aliyu Lawal, Minna Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da shirinta na inganta ayyuka da ƙwarewar gudanarwa a Kamfanin Buga...

Labarai5 days ago

An Ceto Wani Mutum da Ya Fada Kududdufi a Kano

Daga Khadijah Aliyu, Kano   Hukumar kashe gobara ta ceto wani mutum mai shekaru 42, mai suna Sani Uba Kwaru,...

Labarai5 days ago

Tsangayar Kimiyyar Kula Da Lafiya Ta BUK Ta Lashe Zinare A Gasar Kwallon Ƙafa Ta Tsangayu Karo Na 19

Daga Khadijah Aliy, Kano Tsangayar Kimiyyar Lafiya ta Farko (Basic Medical Sciences) ta Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ta...

Labarai5 days ago

Shugaban Majalisar Wakilai Ya Jaddada Muhimmancin Samar Da Ilimi, Lafiya Da Tsaro Ga Al’umma

Daga Ibrahim Suleiman, Zaria Shugaban Majalisar Wakilai ta Nijeriya, Dakta Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa manufar shugabanci ita ce biyan...

Labarai5 days ago

Dan Takarar Gwamnan Sokoto Na ADC Ya Tsalleke Rijiya da Baya Daga Yunkurin Hallaka Shi

Daga Nasiru Muhammad, Sakkwato Dan takarar gwamnan Jihar Sokoto na jam’iyyar  ADC, Hon Mannir Muhammad Dan’Iya, ya zargi jami’an rundunar...

Labarai1 week ago

Mutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya

Mutane aƙalla 64 sun mutu bayan wasu jiragen ƙasa guda biyu masu saurin gudu sun yi karo da juna a...

Labarai1 week ago

Katsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya

Daga Isma’il Adamu  Aƙalla dalibai 64 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Batagarawa, a jihar Katsina, aka garzaya...

Mafi Shahara