Labarai
Jirgin Farko Na Alhazan Jihar Kano Ya Isa Kasa Mai Tsarki
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya kaddamar da jirgin farko na maniyyata aikin hajjin bana a jihar.
Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Gwamna Abba Kabir ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari tare da yin addu’a ga jihar da Najeriya baki daya.
Jirgin na farko na mahajjatan Kano ya tashi ne daidai da karfe goma sha daya da minti arba’in da daya na safiyar yau dauke da jimillar mutane 578, a jirgin sama na Max Air B747 inda suka nufi filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz da ke Jiddah.
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya ce mahajjatan da ke jirgin farkon sun fito ne daga kananan hukumomi hudu na jihar.
A cewarsa, karamar hukumar Gwale na da mahajjata 175, yayin da karamar hukumar Dala ke da alhazai 119, sai karamar hukumar Ungogo tana da alhazai 106, ita kuma karamar hukumar Fagge na da mahajjata 135.
Ya kuma nuna jin jinjinawa Gwamna bisa karamcin da ya yi wa Alhazai da suka hada da tallafin kudin Hajji na Naira 500,000 kowanne, da karin kudin guzuri da ya kai sama da Naira miliyan 367, da karin Riyal 100 da aka bai wa dukkan maniyyatan.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
