Labarai
Jam’iyyar APC Ta Zargi Tsohon Gwamna Tambuwal da Yin Sakaci da Ƙaramar Hukumar Sa
Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato ta zargi tsohon Gwamnan jihar, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, da rashin yin abin da ya dace ga Ƙaramar Hukumar Tambuwal a lokacin da yake kan mulki.
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato, Isah Sadiq Acida, ne ya yi wannan zargi a wani taro da Dandalin Tuntuɓa, Wayar da Kai da Tattara Magoya bayan APC na Tambuwal ya shirya.
Rahoton Rediyo Nijeriya a Sakkwato ya bayyana cewa wannan zargi ya biyo bayan gabatar da rahoton da Kwamitin Bincike na Jihar Sakkwato ya kafa kan mulkin tsohon Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP, inda aka kuma zarge shi da almundahana da kuɗaɗen gwamnati da suka haura naira biliyan ɗari da goma sha bakwai (₦117bn) a lokacin mulkinsa.
Shugaban jam’iyyar ya ce APC a Jihar Sakkwato ta samu gagarumar nasara a Ƙaramar Hukumar Tambuwal, sakamakon sauya sheƙar da kansiloli uku, tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukuma, da kuma wasu manyan jagororin jam’iyyar PDP suka yi zuwa APC mai mulki. Haka kuma, an ba jam’iyyar gudunmawar kuɗi har naira miliyan goma (₦10m) domin ƙarfafa ayyukan wayar da kai da tattara magoya baya.
Da yake jawabi ga mahalarta taron, Mataimakin Shugaban Dandalin, Faruk Dayyabu, ya ce an shirya taron ne domin, a tsakanin sauran manufofi, cin gajiyar yalwar basirar da Allah ya bai wa matasa da al’ummar Ƙaramar Hukumar Tambuwal.
NASIR MALALI
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
