Labarai
NEMA Ta Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Shirye-shiryen Tunkarar Gaggawa
Hukumar Kula da Harkokin Gaggawa ta Ƙasa ta bayyana cewa ingantaccen shiri da martani a lokutan gaggawa na buƙatar ƙaƙƙarfan haɗin kai, da tsare-tsare na gaba a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki.
Wannan ne ya zama jigon wani taron yini guda na Haɗa Kai kan Shirye-shiryen Tunkarar Gaggawa, wanda ofishin ayyukan NEMA na Kano ya shirya tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Harkokin Gaggawa ta Jihohin Kano da Jigawa (SEMA), inda aka gudanar da shi a Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Ayyuka na Ofishin NEMA na Kano, Dr. Nura Abdullahi, ya ce wannan zama ya ba da dama wajen nazari kan darussan da aka koya daga abubuwan gaggawa na baya-bayan nan, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi.
Ya bayyana taron a matsayin wani yunƙuri na duba gaba, domin ƙara ƙarfin bai ɗaya wajen ceton rayuka da kare hanyoyin samun abin rayuwa.
Dr. Abdullahi ya kawo misalin gobarar Kasuwar Singer a Kano a matsayin shaida kan yadda shiri da haɗin kai ke inganta sakamakon martani, inda ya yaba wa Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, hukumomin tsaro, jami’an lafiya, masu sa kai na al’umma da kuma abokan hulɗa daga kamfanoni masu zaman kansu bisa gaggawar da suka yi.
Da yake sanar da buɗe taron, Babbar Sakatariya ta Ma’aikatar Ayyukan Jin-ƙai ta Jihar Kano, Hajiya Amina Yar’gaya, ta jaddada buƙatar ci gaba da haɗin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki. A nasu bangaren kuma, jami’an SEMAs na Kano da Jigawa sun bayyana ambaliya a matsayin babbar barazana gabanin daminar shekarar 2026.
Taron, wanda aka yi wa taken “Bita kan Shirye-shiryen Tunkarar Gaggawa na 2025 da Tsara Dabarun Martani don 2026,” an shirya shi ne domin yin bitar ayyukan shirye-shirye da martani na gaggawa da aka aiwatar a shekarar 2025, tare da samar da tsare-tsaren dabaru na shekarar 2026.
ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
