Kasuwanci
Jam’iyyar APC Ta Tabbatar Da Gwamna Ganduje Ya Ajiye Aiki
Jam’iyyar (APC) ta tabbatar da murabus din shugabanta na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ba tare da bata lokaci ba.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana cewa Ganduje ya mika takardar murabus din ne ta wata wasika da ya aikewa kwamitin ayyuka na kasa (NWC) ta hannun sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa murabus din nasa ya zama dole domin ya samu damar gudanar da wasu al’amura na gaggawa da suka shafi kashin kansa.
Tuni dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci mataimakin shugaban kasa (Arewa) Alh Ali Bukar Dalori da ya karbi ragamar mulki har zuwa lokacin da za a gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa domin zaben sabon shugaba.
Hukumar NWC ta nuna jin dadin ta ga irin gagarumar gudunmawar da Ganduje ya bayar da kuma fitaccen tarihin hidima tare da yi masa fatan samun nasara a ayyukansa na gaba.
REL/IBRAHIM SHEHU/Bello WAKILI
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
