Kasuwanci
Kwamitin Sasanta Manoma Da Makiyaya Ya Fara Rangadi A Jigawa
Kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar Jigawa ya yi kira ga kananan hukumomin jihar da su ci gaba da hana keta haddin filayen kiwo da hanyoyin shanu wato burtali ko labi da kuma bangaran hanyoyi domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin manoma da makiyaya a yankunansu.
Shugaban kwamatin Dr Salisu Abdullahi Dan Malikin Ringim ne ya yi wannan kiran a yayin wani rangadin sanin makamar aiki a kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar na kare rayuka da dukiyoyin al’ummarta musamman manoma da makiyaya ta hanyar samar da kyakkyawar alaka a tsakanin bangarorin biyu.
Dr Salisu Abdullah wanda Sakataren zartarwa na hukumar, ya yi nuni da cewa, Gwamna Umar Namadi ya bullo da shirye-shirye daban-daban na tallafa wa manoma da makiyaya su shiga sana’o’in noma domin dogaro da kai da ci gaban tattalin arziki.
A nasu jawabin shugaban karamar hukumar Auyo Malam Binyaminu Kafur da na Kafin Hausa Malam Abdullahi Nalayi sun bayyana kudirinsu na tallafawa kwamitin sulhu na rikicin manoma da makiyaya a kokarin da yake yi na wanzar da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya a yankunansu.
Usman MZ
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
