Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Buhunan Abinci 36,000 Ga Jihar Borno

Published

on

Gwamnatin tarayya ta baiwa gwamnatin jihar Borno tallafin buhunan abinci dubu talatin da shida da dari biyu da goma sha hudu masu nauyin kilogiram hamsin.

Da take gabatar da kayayyakin ga Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Zulum, Darakta Janar ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa NEMA, Hajiya Zubaida Umar ta ce kayayyakin na daga cikin  tan dubu arba’in da biyu  na hatsi da aka fitar daga runbun gwamnati.

Shugabar hukumar wacce darakta janar na shiyyar Arewa maso Gabas, Malam Yakubu Sulieman, ya wakilce ta, ta bayyana cewa bada tallafin kayan abinci na daga cikin shirin rage tasirin tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a yankin.

Shugaban kasa ya amince da fitar da kayayyakin abinci har ton 42,000 daga runbun gwamnatin tarayya da ke karkashin kulawar ma’aikatar noma da samar da abinci ta, a don haka mun zo ne domin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar Borno inda za ta  raba ga wadanda suka cancanta”.

A jawabinsa, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya jinjinawa  gwamnatin tarayya bisa wannan karamci ga al’ummar jihar, musamman wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Ya kuma baiwa shugaban kasa da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa tabbacin cewa za a raba kayan abincin da aka bayar ga marasa galihu a jihar.

Ina kuma tabbatar muku da cewa ba za a samu karkatar da kayayyakin a jihar Borno ba, za a raba bisa cancanta ga al’ummar jihar.” Inji Zulum.

Gwamna Zulum ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa bada gudunmawa a yunkurin da gwamnatin sa ke yi na sake tsugunar da wadanda rikici ya daidaita.

Shi ma a nasa jawabin,  Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar SEMA, Dokta Muhammed Barkindo ya ce za a ba da fifiko ga gidaje suka rasa mahaifinsu da marasa lafiya da kuma masu fama da lalurar nakasa.

Kayayyakin da aka bayar sun hada da buhunan Masara 11,880, buhunan dawa 19,440 da buhunan Gero 5,130.

 

Dauda Iliya 

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara