Labarai
Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar ‘yan jaridu a aikin Hajjin 2024.
An bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na kaddamar da kwamitin gudanar da aikin Hajji na shekarar 1445AH/2024 a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da ke kwaryar birnin jihar.
Taron ya samu halartar ma’aikatan kafafen yada labarai da za su rika ba da rahoton abubuwan da ke gudana yayin aikin Hajji wanda dubban maniyyata daga Najeriya da ma sauran sassan duniya baki daya ke halarta.
Shuaibu, wanda a halin yanzu shi ne sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kware a harkar yada labarai da sadarwa.
Ya kuma taba zama tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) Correspondents Chapel reshen jihar Kano, da kuma wakilin jaridar This Day.
Nadin da aka yi masa a matsayin shugaban tawagar kafafen yada labarai wani gagarumin ci gaba ne, wanda ake sa ran zai yi amfani da kwarewarsa wajen tafiyar da harkokin yada labarai na aikin hajji.
Sama da maniyyata 3,000 ne daga jihar Kano ake sa ran za su halarci aikin Hajjin 2024.
A ranar 15 ga watan Mayu ne daidake sa ran fara jigilar maniyyata daga kasar nan zuwa kasa mai tsarki.
Gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali da nasara ga dukkan maniyyata, kuma nadin Shuaibu na daya daga cikin muhimman ayyukan.
Khadija Aliyu
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
