Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka
A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu manyan kamfanoni da suka yi fice a fannin dabarun bincike da samar da kayan aikin gona na zamani domin bunƙasa harkar noma a jihar.
Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Ya yi bayanin cewar, an ƙulla wannan yarjejeniyar haɗin gwiwa ne a wani zaman tattaunawa da aka yi a birnin Washington DC na Kasar Amurka tsakanin tawagar ƙwararru daga Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi da kuma wakilan shugabannin kamfanonin da abin ya shafa.
A cewar sa, tattaunawar da ta gudana tsakanin ɓangarorin biyu ta ta’allaƙa ne kan yadda za a samar da kuma bunƙasa dabarun noma tare da shigar da matasa cikin harkar noma domin ganin an ɗaga matsayi da inganta rayuwar al’ummar jihar Jigawa ta hanyar noma.
Hamisu Mohammed Gumel ya yi nuni da cewar, daga cikin kyawawan sakamakon da wannan tattaunawar ta haifar shine ƙuduri na haɗin gwiwa da aka zartas na samar da wani shiri da a cikinsa za a siyo tarakta guda 300.
Yana Mai cewar nan bada jimawa ba za’a kawo su don ci gaba da inganta harkar noma a jihar ta Jigawa.

Ya ce wannan zai taimaka matuƙa wajen bunƙasar samun amfanin gona mai kyau da inganci a tsakanin ƙananan manoman jihar.
Hamisu Mohammed ya ce a ƙarƙashin wannan shiri ana sa ran za a horas da matasa sama da dubu daya da dari biyu kan harkar kasuwancin sayarwa da ba da hayar kayan aikin gona da kuma sarrafawa tare da gyaran taraktoci da sauran na’urorin aikin da za a samar.
Babbar manufar wannan shiri ita ce jawo matasa su shiga cikin harkar noma, wanda a yau ita ce hanyar samar da isasshen abinci da bunƙasar tattalin arziki a jiha da kuma ƙasa baki ɗaya.
Kazalika, yace hakan wani ɓangare na manufofin da Gwamna Umar Namadi ya ƙuduri aiwatarwa don inganta fannin noma da sauran fannonin rayuwa a Jigawa da ya zayyana a cikin ƙudurori 12 na gwamnatinsa.
Da yake magana kan ƙulla wannan haɗin gwiwa, Gwamna Umar Namadi ya ƙara jaddada muhimmancin yin amfani da dabaru da kayan aikin gona na zamani tare da jawo matasa cikin harkar, domin ta hakan ne za a tabbatar an inganta wannan fannin na noma a nan gaba.
Namadi, ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafawa manoma, musamman matasa da a yanzu suka fara ganin muhimmancin wannan fanni, ta hanyar samar da kayan aiki da dabarun noma na zamani don ci gaban al’umma.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
