Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Jigawa Ta Bada Takardar Kama Aiki Ga Malaman Makarantu Sama Da 3000

Published

on

 

Gwamna Umar Namadi ya bayar da takardun kama aiki na dindindin ga malaman makarantu 3,143, tare da daukar ma’aikatan wucin gadi 2,445 a jihar.

Da yake jawabi a wajen bikin bayar da takardun kama aikin da aka gudanar a dakin taro na Malam Aminu Kano Triangle da ke Dutse, ya bayyana cewa, wannan gagarumin aikin na daga cikin tsare-tsare na samun nasarar aiwatar da manufofinsa guda 12.

Ya bayyana cewa babu wata manufa ta gwamnati da za a iya aiwatar da ita yadda ya dace ba tare da isasshen horo da kwararrun ma’aikata ba.

Ajandarmu guda 12 da aka tsara don ganin jihar Jigawa ta bunkasa sun hada da samar da ilimi mai inganci ga daukacin yara a jihar, kuma don samun nasarar haka ya zama wajibi mu kara samar da kwararrun malamai.”

Ya ci gaba da bayanin cewa, a kokarin cimma burinsu na samar da muhimman ayyukan kiwon lafiya ga daukacin ‘yan jihar, magance yawaitar mace-macen yara da mata masu juna biyu, samar da lafiyar al’umma  da walwala, gwamnatin jihar ta tura  dalibai sama da 120 zuwa  kasashen Cyprus da Indiya domin karatun aikin likitanci.

A cewarsa, gwamnati mai ci ta kaddamar da gina makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta naira biliyan 5 da rabi, inda a yanzu ta bayar da aikin yi ga ma’aikatan lafiya 1,005 da suka hada da likitoci da kananan ma’aikata.

Gwamnan ya yi nuni da cewa, noma na daya daga cikin muhimman sassa na ajandarsa guda 12, wanda aka kudiri aniyar samar da ayyukan yi, kawar da fatara, samar da abinci, da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Haɓaka amfani da fasahar noma ta zamani da samar da kayan aikin gona na zamani da araha ga manoma yana da matuƙar mahimmanci wajen cimma burin da aka sa a gaba, kuma bisa la’akari da hakan a yau muna gabatar da tayin aiki ga ma’aikatan aikin gona na wucin gadi 1,440 a ƙarƙashin shirinmu mai suna J-Agro. ” Inji Gwamnan.

A nasa jawabin shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa ya ce malaman da suka yi aikin koyarwa na wucin gadi na tsawon shekaru biyu a jihar an basu takardar aiki na dindindin  bayan cin jarrabawar da suka yi.

Ya ce, dukkanin malaman 3,143 an basu aikin ne bisa cancanta, ya kuma ba da tabbacin cewa, dukkansu suna da kwarewar da ta dace.

Farfesa Haruna Musa ya ce, hukumar za ta ci gaba da sanya ido kan sabbin ma’aikatan da aka dauka, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen korar duk wanda ya kasa bin ka’idojin daukar ma’aikata.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara