Connect with us

Labarai

Hajjin Bana: Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Jigilar Maniyyatan Jihar

Published

on

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kaddamar da jigilar maniyyata kashin farko  zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin 2024.

Gwamna Dauda Lawal wanda ya kaddamar da fara gudanar da aikin a sansanin Alhazai na jihar da ke Samaru Gusau, babban birnin jihar, ya kuma yi kira ga alhazan  da su  bin dokokin Saudiyya sau da kafa, kuma su guji duk wani abu da zai iya bata sunan su da na jiharsu da ma Najeriya  baki daya.

Dauda Lawal ya kuma bukace su da su yi amfani da kudaden su yadda ya dace, tare da gujewa sayayya barkatai.

Ya sanar da bayar da kykyautar Dala dari ga kowane mahajjaci daga jihar, inda  ya kara da cewa,  ita ma mai dakinsa Hajia Huriya Dauda Lawal ta shiryabayar da irin wannan kyauta ga Alhazan.

Gwamnan ya kuma yi kira ga maniyyatan jihar da su yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya a jihar Zamfara da yankin Arewa da ma Najeriya baki daya.

Tun da farko, a jawabinsa na maraba, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, Malam Musa Mallaha, ya ce maniyyata dubu daya da dari bakwai da sha biyu ne ake sa ran za su yi aikin Hajjin bana.

Jirgin farko na jihar ya kunshi mahajjatan daga kananan  hukumomi hudu na jihar wadanda suka hada da Bakura, Bukuyum, Gummi da Shinkafafi, kuma ana sa ran zai tashi daga filin jirgin saman Sultan Abubakar III da sanyin safiyar yau Laraba 29 ga watan Mayu, 2024.

Sani Haruna Dutsinma

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara