Connect with us

Fasaha

Gwamnatin Jigawa Da Bankin Duniya Sun Dauki Nauyin Dalibai 500 A Fannin Fasahar Zamani

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, ta dauki nauyin dalibai sama da 500 a wani mataki na tsara makomar matasa a fannin fasahar zamani.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da shirin da kuma mika takardun shaidar karatu ga wadanda suka ci gajiyar shirin fasahar zamani na Innovation Development and Effectiveness in the Acquisition of Skills (IDEAS) a Jihar Jigawa.

Malam Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafawa matasa ta hanyar kirkire-kirkire a fannin fasahar zamani da kuma koyon sana’o’i don habaka tattalin arziki.

A yau, mun kammala horar da dalibai 240 da suka koyi yadda za su bunkasa  harkokinsu na kasuwanci don tabbatar da ci gaba mai dorewa,” in ji gwamnan.

Haka kuma, a yau muna mika takardun shaidar karatu ga dalibai 550 da suka sami guraben karatu ta hannun Hukumar Samar da Ayyuka da Taimakon Matasan Jihar Jigawa, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, Arms of Ideas, da gwamnati.”

A cewarsa, wadannan dalibai da suka sami guraben karatu a Jami’ar Baze za a horas da su a fannonin fasahar zamani da ke taka muhimmiyar rawa a kasuwannin duniya.

Gwamna Namadi ya bayyana cewa karkashin wannan shiri, Gwamnatin Jihar Jigawa da Bankin Duniya sun saka hannun jarin sama da Naira miliyan 100 domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi da koyon sana’o’i.

Wannan kudade hadin gwiwa ne tsakanin Bankin Duniya da Gwamnatin Jihar Jigawa. Bankin Duniya ya bayar da Naira miliyan 85, yayin da gwamnatin jihar ta bayar da Naira miliyan 50, kuma an riga an biya kudaden gaba daya.”

Ya kara da bayanin cewa shirin zai ba dalibai damar koyon akin binciken sirri, (Artificial Intelligence), da fasahar blockchain, binciken kasuwanci (Business Intelligence), da tsaron yanar gizo (Cybersecurity), da sauransu.

Baya ga horon fasahar zamani, gwamnan ya kuma sanar da kammala horas da matasa ‘yan kasuwa 240 da suka samu horo kan hanyoyin bunkasa kasuwancinsu. Ya kara da cewa kowannensu zai samu tallafin jari na Naira 50,000 domin fadada kasuwancinsu da kuma tabbatar da dorewarsa.

Saboda haka, Gwamna Namadi ya bukaci daliban da su yi amfani da wannan dama yadda ya kamata, tare da tabbatar musu da karin tallafi ga wadanda suka yi fice a karatunsu.

Ina bukatar ku yi kokari don cimma wannan buri. Duk wani dalibi da ya kammala karatu da Upper Credit ko Distinction zai samu sabuwar kwamfutar tafi-da-gidanka (laptop) domin tallafa masa!”

Ya sake tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa ga fannin fasahar zamani,  da karfafawa matasa tattalin arziki a Jihar Jigawa, tare da alkawarin gabatar da karin manufofi da shirye-shirye don inganta rayuwarsu da kuma bunkasa sana’o’insu.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

 

Labarai

Labarai4 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara