Ilimi
Gwamnatin Jigawa Da UNICEF Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Shirin Kare Hakkin Yara
Gwamnatin Jihar Jigawa da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun rattaba hannu kan shirin aiki na shekaru 3 (2025-2027) da nufin inganta kare hakkin yara da mata, tare da tabbatar da rayuwarsu da ci gabansu a cikin jihar.
Taron sanya hannun, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse, ya samu halartar Gwamna Malam Umar Namadi da kuma Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah, tare da wasu manyan baki.
A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya jaddada kyakkyawar alakar da ke tsakanin Jigawa da UNICEF tun daga kafuwar jihar a shekarar 1991.
“Kamar yadda na saba fada, UNICEF ita ce tsohuwar abokiyar cigaban jihar Jigawa, wacce ke ci gaba da tallafa wa jihar tun bayan kafuwarta a 1991” in ji Gwamna Namadi.
Malam Umar Namadi ya gode wa UNICEF bisa jajircewarsa wajen samar da kudade da aiwatar da shirye-shirye da suka haifar da ci gaba a fannoni daban-daban.
“Yayin da muke sanya hannu kan wannan shirin na shekaru uku, ina so in sake tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa za ta aiwatar da shi gaba daya, tare da yakinin cewa tare da hadin gwiwarmu za mu cimma burin da aka sanya a gaba.”
Ya jaddada cewa kowane yaro a Jihar Jigawa yana da damar samun kariya, tsira da rayuwa, bunkasa, samun ilimi, da kuma cika burinsa a cikin iyali mai karfin tattalin arziki da kuma kyakkyawan yanayi.
Ya kara da cewa jihar za ta samar da dukkanin yanayin da ake bukata domin aiwatar da shirin, ciki har da sabunta dokoki, samar da kudade, da inganta hanyoyin hadin gwiwa domin tabbatar da ingancin shirin.
A nasa jawabin, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah ya jinjinawa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa jajircewarta wajen inganta rayuwar yara da mata.
Farah ya bayyana cewa, duk da karancin tallafin kudi daga masu bayar da gudunmawa a duniya, Jigawa ta nuna kwarewa da kirkire-kirkire wajen bunkasa ci gaba.
“Sanya hannu kan wannan shirin ya sake tabbatar da hadin gwiwarmu, wanda ke da matukar amfani ga yara da iyalai a Jihar Jigawa,” in ji shi, yana mai bukatar gwamnati ta kara ware kudade don bunkasa wadannan fannoni domin dorewar shirye-shiryen, ba tare da dogaro da tallafin kasashen waje ba.
Rediyo Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Namadi ya umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar da shirin.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27