Labarai
Funtua: An Bukaci Tallafi Ga Marayu da Yara Marasa Galihu
Shugaban Kwamitin Tallafawa Marayu na Riyadissalihin da ke Funtua, Alhaji Lawal Mekaji, wanda aka fi sani da Madugun Kasuwar Funtua, ya yi kira ga masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wa marayu da yara marasa galihu a cikin al’umma.
Alhaji Mekaji ya yi wannan kira ne yayin rabon kayan sawa da kayan abinci ga wata cibiyar marayu a Funtua, Jihar Katsina, a matsayin wani bangare na ayyukan da ake gudanarwa domin tunawa da watan Ramadan mai alfarma.
Ya ce kula da marayu hakki ne na kowa da kowa, tare da kira ga al’umma da su yi amfani da wannan wata na Ramadan wajen nuna tausayi da karamci ga marasa galihu.
A cewarsa, an yi wannan tallafi ne domin rage radadin halin da yara ke ciki tare da tabbatar da cewa sun samu damar cin gajiyar albarka da farin cikin watan azumi.
Da yake mayar da jawabi a madadin gidauniyar, Sakataren ta, Bashir Muhammad King, ya shawarci wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kayayyakin yadda ya dace.

Haka kuma ya gode wa masu bayar da tallafi da masu aikin sa kai da suka bayar da gudunmawa wajen ganin shirin ya yi nasara, inda ya bayyana tallafin nasu a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma mai tasiri.
A nasa jawabin, Daraktan gidauniyar, Sheikh Yusuf Lawal, wanda shi ne Sarkin Kara na Funtua, ya jaddada kudirin kungiyar na inganta rayuwar marayu a yankin.
Ya bayyana shirin gina makaranta da kuma ginin dindindin na marayu a Funtua domin samar musu da ingantaccen ilimi da matsuguni.
Sheikh Lawal ya yi kira ga attajirai, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kasa da kasa da su hada hannu da gidauniyar wajen cimma manufofinta, yana mai jaddada cewa dorewar tallafi zai taimaka wajen samar wa yaran makoma mai kyau.
Magaji Yakawada
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
