Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Jinjinawa Matasa Bisa Yada Manufofin Gwamnatin Jihar Jigawa

Published

on

Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya kaddamar da taron yini biyu kan dandalin sada zumunta wanda cibiyar manema labarai ta Danmodi Media ta shirya.

Taron wanda ke gudana a cibiyar bunkasa ayyukan yi, ya tara matasa maza da mata daga kananan hukumomi 27 dake fadin jihar wadanda suke amfani da kafafen sadarwa na zamani.

A jawabinsa, Gwamna Umar Namadi ya jaddada jin dadinsa ga matasa da suke yada manufofin gwamnatin jihar Jigawa.

Ya gode musu bisa kokarinsu da jajircewarsu wajen kare muradun gwamnati.

A madadina da duk wadanda suka tsaya takara a shekarar 2023, muna mika godiyarmu ga matasan kafafen sada zumunta na zamani bisa kokarinsu da jajircewarsu na samun nasara,” inji gwamnan.

Namadi ya kuma gargadi matasa da su guji yin amfani da su da kuma yada abubuwan da ba su dace ba da ka iya keta mutuncin mutane.

Ya yaba da irin gudunmawar da matasan suka bayar wajen samun nasarar gwamnati tare da ba su tabbacin karrama su busa wannan kokari da suke yi.

Gwamna Namadi ya kuma mika godiyarsa ga wadanda suka shirya taron na wayar da kan matasa kan yadda ake amfani da kafafen sadarwa na zamani.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai9 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara