Labarai
Za Mu Yaki Ayyukan Ta’addanci A Jihar Kano – Sabon Kwamishina
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano CP Salman Dogo Garba, ya fara sintiri a yankunan da ‘yan daba suka sake kunno kai a wasu sassan birnin Kano, tare da tabbatar wa mazauna yankunan kudurinsa na wanzar da zaman lafiya.
CP Dogo Garba ya nemi hadin kan shugabannin al’umma da jami’an ‘yan sanda na yanki (DPOs) don tsara dabarun yakar wannan barazana da kuma dawo da tsaro.

Ya jaddada cewa tsaro hakki ne ya rataya a wuyan kowa, don haka ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wata barazana da ka iya kunno kai ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su ko kuma ta lambobin gaggawa.
CP ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, kuma ana kokarin kamo masu aikata laifin da masu daukar nauyinsu.
Ya yaba da goyon bayan mazauna yankin masu son zaman lafiya, inda ya bukaci a ci gaba da ba da hadin kai.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
