Labarai
Shugaban Kasa Ya Jajanta wa Yan Kasuwar Da Gobara Ta Shafa A Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a yi taka tsantsan tare da bin muhimman matakan tsaro don hana barkewar gobara da sauran hadurra.
Shugaban ya bayar da wannan shawarar ne a lokacin da yake jajanta wa ‘yan kasuwa a kasuwar Karu da ke cikin babban birnin tarayya wanda gobarar ta shafa.
Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Cif Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu, ta ce shugaban kasar ya ba wa wadanda gobarar ta shafa tabbacin samun cikakken goyon bayan gwamnatinsa.
A yammacin ranar Alhamis ne gobara ta tashi a kasuwar inda ta lalata dukiya da sauran kayayyaki masu daraja.
Bello Wakili/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
