Fasaha
Daliban mu Na Daf da Fara Kera Motoci – Farfesa Katsayal
Dalibban Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya dake Daura na daf da fara Jirage da Motoci
Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ne ya bayyana haka lokacin da yake magana da Radio Nijeriya Kaduna a ofishinsa na Daura.
Ya kara da cewa Jami’ar Sufurin da Gwamnatin Tarayya ta Samar na da manufar Samar da dalibbai masu hazaka da zasu kasance masu kirkire kirkire da manufar ganin ana yaye dalibbai da zasu dogaro da kansu dama taimakawa wajen habakar tattalin arzkin kasa.
Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ya Kara da cewa baya ga ilmantar da dalibbai Jami’ar tsaye take wajen ganin sun Samar da dalibbai masu tarbiyya da zasu kasance abin alfahari cikin al’umma.
Hakama Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa yanzu haka dalibbai da suka fara karatu a Jami’ar na samun ingantaccen Ilmin Kimiyya da Fasaha da zasu kasance masu kirkire kirkire da nan gaba zasu kasance masu kawowa wannan kasa habakar tattalin arzkin baya ga dogaro da kansu da samarwa dinbin al’umma ayukkan yi.
Idris Kaurar Namoda
-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoƊaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano
