Connect with us

Labarai

Cocin Katolika Ya Yi Bikin Ma’aurata 21 A Neja

Published

on

Bishop na Cocin Katolika da ke  Kontagora, Babban Rabaran Bulus Yohanna ya gudanar da bikin aure ga ma’aurata ashirin da daya a jihar Neja.

A lokacin da yake jawabi yayin bikin daurin aurea cocin St. Mark Catholic da ke Nsanji Nkoso a karamar hukumar Magama ta jihar Neja,  Bishop din ya bayyana cewa, bai kamata masoya na zama tare ba har sai coci ya tabbatar da su a matsayin ma’aurata bayan an biya sadaki da kuma bin ka’idoji.

A cewar Most Reverend Bulus Yohanna “mafi yawansu sun fi dogaro da auren gargajiya wanda a baya ya basu damar zama tare. “Kuma muna bukatar mu tabbata cewa babu wani daga cikinsu da aka tilastawa”.

Dole ne mu ƙarfafa su  su yi abin da ya dace musamman a matsayinmu na ’yan Katolika. Da wannan albarkar aure, wadannan ma’aurata ashirin da daya sun yi aure a bisa doka kuma a hukumance”.

Bishop Yohanna wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Neja, ya kara da cewa, aure alkawari ne na rayuwa wanda ya kamata a gina shi bisa soyayya

A nasa jawabin Rev. Fr. Francis Yasak Joshua,  ya bayyana cewa ma’auratan su 21 sun kammala ibadar aurensu na gargajiya musamman biyan kyaututtuka ga amare, ya ce an yi musu nasihar aure na tsawon watanni uku.

Su dai wadannan ma’aurata sun kasance tare na tsawon lokaci ba tare da coci ya tabbatar da auren nasu ba, inda wadanda suka fi dadewa tare su ne wadanda suka kwashe shekaru 24 a matsayin ma’aurata,  yayin da masu mafi karancin shekaru kuma su ne wadanda suka shekara daya.

Daya daga cikin wadanda suka dauki nauyin ma’auratan Lydia Ishaya ta bayyana jin dadinta inda ta ce “na yi matukar farin ciki,  ina kuma rokon Allah Ya  albarkaci aurensu”.

Wasu daga cikin ma’auratan sun bayyana jin dadinsu bisa yadda cocin ya tabbatar da aurensu a hukumunce.

Wasu daga cikin ma’auratan, Mista da Misis Cyprian Uche da suka kwashe shekaru 22 suna rayuwa tare, sun ce yanzu haka suna da ‘ya’ya 5, inda wasunsu sun  kammala manyan makarantun gaba da sakandire, sauran kuma suna makarantar sakandare.

Daga Aliyu Lawal

Labarai

Labarai11 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara